.
KE KIKA JA (part 05)
Nayi nisa cikin barci mai dadi harna ajikke bargo gefe saboda iska mai dadi dake kadawa a harabar gidan, ita kuma khadija tana ciki ta gaza samun barci saboda tsananin tunanina da takeyi duk ta rintse ido ni take gani, ta mike tana dube-duben dakin taga littafaina na makarantar muhammadiyya take cewa a zuciya "ashe yaronan malamine?"...... Tashi nayi zubud daga barci sakamakon karan loud speaker alaman lokacin sallah ya kusa, na mike nayi alwula sannan nashiga daki naga khadija a zaune nace "khadija ba barcine?" tace "ai..... Ai.... Ai na rigaka tashi" toh tashi kiyi alwula dan ummana ta kusa tashi na nuna mata bayi na bata torch light hmmm....... Tana shiga ta dawo a guje tace "wlh naga wani abu, mai idanuwa masu walkiya" na karbi torch ina zuwa naga ashe kyanwar makwabta tashigo bayin sai na korata, ita kuma ta koma a tsorace ta fito tayi alwula.... Inaji ummana tana kokarin bude dakinta sai nayi saurin tura khadija daki na kulle dakin da makulli nace kada tayi 6uruntu, ni kuma na tafi masallaci.... misalin karfe 6:12am lokacinda aka gama sallah jama'a suka taru gaban motar khadija, ina fitowa aka tareni "JARMA MOTAR WAYE?? KO KANIN MALAM KABIRU YAZO????" nace "yada kuka ga wannan mota haka naganta saboda haka kowa ya tafi!!!" na wuce sulup-sulup na shige daki nace "toh yanxu xaki tafi kafin umma ta fito amma......(sai na kama dube-dube)" can sai naga malum-malum da nake sakawa lokacin sanyi, take na daukota nace "ungo saka wannan ni ina waje" tayi shiri tasa malum-malum da hula Qube iwa alhajin gaske haba!!!! Tana fitowa jama'a suka taru nayi maza nace "kada ki kuskura kiyi mgn" ta ciro kudi ta mika masu tashige mota taja muka tafi zuwa gidansu..... Loading Part 06......
No comments:
Post a Comment