KE KIKA JA (part 04) sweet love Hausa Novels By Jarma Ubandiya KNT


.
KE KIKA JA (part 04)



Mun gama BDparty, kowa yayi rawa an rakarkashe, itako driver tana can jikin motarta ta nade hannu tan kallona.... Bayan mun kammala sai na soma tunanin abinda yasa tazo nan, na matsa kusada ita ina gyara rigana, ina cewa "madam driver yadai?"(na daga mata gira) tace "me kuwa"(ta kara gyara tsayuwa) nace "wai meya kawoki safara ke kadai?" ta lalabi keya tace "kawai tunda nazo garinnan naji anata ambaton safara, wai ana chasu da dare, ni kuma nace yau sai nazo na ganewa idanuna" na lalabi wuya nace "gud, kina gane gida yanxu?" ta rike baki tace "tap!!! Banfa taba fita yawoba sai yau, amma muje gidanku in kwana acan" keh!!!! Shine abinda ya fito bakin yayinda na dafe kaina, daga can king asa yace jarma muje gida mana!! Nace "go ahead" sai na canja shawara nace "driver muje gidanmu" ta zazzaro mani idanunta masu bala'in kyau tace "nifa ba sunana driver ba, khadija sunana" na kara daga mata gira na daure kekena kan roof din mota tajamu a guje na nuna mata hanya...... Ji nayi dogon hancina ya kwale a gaban mota sakamakon dogon birki da tayi yayin tsayawa kofan gidanmu nace "yaaashhh!!!! Wat f4ckin is dis" ta tinsire da dariya tace "sorry bicycle man" na harareta na fito na sauke kekena itama ta biyoni baya, muna isa tsakiya gidanmu na tsaya cak....... Na girgiza kai nace "hmmm akwai aiki" ta jayoni baya ta tambiyeni "yadai?" na mike dakina na bude nace "nan xaki kwana" tace "to kaipah?" ba ruwanki nayi mata hannu alaman dakatarwa, na dauko bargo na baza kofan dakina na kwanta.. Saida safe yayinda na lullube da bargo, ita kuma ta koma cikin daki ta kwanta.... Part 05 loading...

SHARE THIS

No comments:

Post a Comment