RAYUWAR SAMARI DA 'YAN MATA NA CIKIN WANI YANAYI


..,
1- Ina Mamakin Yanda Kowane Namiji Idan Ya Tashi
Aure Wai FARAR MACE Yake So Kuma Mai Kyau. Malam
Kai FARI Ne Ko KYAWUN Ne Da Kai ???
2-Idan Da'ace MATAN Zasu Cire Kwadayi Da Son Abin
Duniya Suma SuCe Dole Sai Fari Dogo Mai Hanci Mai
Kyau Suke So Su Aura Don Allah MAZA Nawa Ne Kenan
Zamu AURU 5% Ko 10% ???
3-Sannan Sai Kaga Namiji Ya Dage Wai Shi Sai Yar Mai
KUDI Zai Aura Toh Kai Dan Mai KUDI Ne ???
4- Kema MACE Ki Dage Waike Sai Mai Kudi Zaki Aura
Toh
A Lokacin Da Mahaifin Ki Yayi Auren Farare Bugun
Abuja
Nawa Yake Dasu ???
5- Saikaga Namiji Ya Dage Wai Shi Ba Zai Yi Aure Ba
Sai Yayi KUDI Tambayata Anan Shine Kasan Lokacin Da
Zaka Yi Kudin ??? Kuma Nawa Ne Zaka Mallaka A
Duniya ???
6- Haba Yan Mata Wai Kema SaiKi Dage Wai Sai Anyi
Miki LEFE Akwati 12 Watama Wai Saidai 14 Yan Mata
Koma Gida Ki Tambayi Mahaifiyar Ki Akwati Nawa
Tsohon Ki Ya Kawo Mata Lokacin Da Zai Aureta ???
Watakila Ma KWALLA Ce Guda 1 Ko 2.
7- Yan Mata Kun Jefa SAMARI Akan Dole Sai Sun Yi
KUDI Ko Ta Wane Hali Sannan Zaku Aure Su Wanda Ta
Hakan Wasu Samarin Sun Koma 419 Wasu Sata Kawai
Don Su Auri Fararen Mata Masu KYAU.
8- MuKuma MAZA Mun Jefa Mata A Bala'i
Na BLEACHING SHIGAR BANZA NUNA TSARAICI
BARA'A GA DOKAN ALLAH
Kawai Don Su AURI Namiji Mai Kudi Mai Kyau.
9- SAMARI Da YAN MATA Mu Ajiye Burukan Dake
Makare Azuciyoyin Mu Mu Taru Mu
Rufawa Juna Asiri
10- MAZA Da MATA Mu FARGA !!!
WALLAHI BA HAKA IYAYEN MU SUKA
RAYU BA......

No comments:

Post a Comment